logo

HAUSA

Xi ya bukaci a ci gaba da inganta hadin kai tsakanin kabilu a dukkan zuri’o’i
Rediyo
  • In Ba Ku Ba Gida
  • Sin da Afirka
  • Duniya A Yau
  • Wasannin Motsa Jiki
  • Allah Daya Gari Bambam
  • Yao Yanmei ta nuna himma da hikima don rubuta almara ta farfado da karkara

    A filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Beijing na kasar Sin, a cikin manyan fostocin da ke gungurawa a kan babban allo, ba wata shahararriyar tauraruwa mai jan hakulan mutane ake nunawa ba, ba kuma wata attajira da ta samu gagarumar nasara ba, sai dai wata mace ta gari daga dangin manoma, wadda ta nuna himma da hikima don rubuta almara ta farfado da karkara. Ita ce Yao Yanmei mai shekaru 33, shugabar kamfanin kimiyya da fasaha kan sha’anin noma na Jinghe.

  • Ziyarar Kande Gao da tawagarta a kasashen yammacin Afirka uku

    Kande Gao, mataimakiyar shugaba ce ta sashin Hausa na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, wadda ta jagoranci wata tawaga dake kunshe da mutane hudu don ziyartar kasashen Nijar, Ghana da Najeriya, daga karshen watan Agusta zuwa farkon watan Satumba na shekarar da muke ciki, ciki har da Murtala Zhang, da Tasallah Yuan. A yayin zantawar Murtala Zhang da ita, malama Kande Gao ta yi karin haske kan ziyarar da suka yi a kasashen uku, da abubuwan da suka burge ta a yayin ziyarar, kana, ta bayyana kyakkyawan fatanta gami da mika gaisuwa ga jama’ar kasashen uku...

  • Ya zama wajibi a ci gaba da karfafa tushen aikin gona

    Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, yawan amfanin hatsi na kasar Sin ya karu akai-akai tun daga shekarar 2012. Yayin da a shekarar 2015, yawan hatsin ya haura tan miliyan 650, wata muhimmiyar nasara ce da kasar ta ci gaba da kiyayewa tsawon shekaru tara a jere. Ya zuwa shekarar 2023, yawan hatsin da kasar Sin ta samu kan kowane mutum ya kai kilogiram 493, adadin da ya zarce matsakaicin adadi na duniya tsawon shekaru a jere. Duk da illolin da bala'u min indillahi da sauran kalubale suka haifar a bana

  • Nijeriya Ta Samu Lambobin Yabo 7 A Wasannin Nakasassu Ta Bana

    Nijeriya ta kammala gasar wasannin nakasassu ta shekarar 2024 a birnin Paris da samun lambobin yabo bakwai da suka hada da zinare biyu, da azurfa uku, da tagulla biyu, inda ta zo ta 40 cikin kasashe 83.

  • Yadda ake kokarin saukaka rayuwar mutane masu bukatar musamman a Sin

    Yadda ake tabbatar da rayuwa mai sauki ga nakasassu da mutane masu bukatar musamman, ya kan nuna matsayin ci gaban al'ummar wata kasa. Don tabbatar da ci gaban wannan bangare, kasar Sin ta kaddamar da sabuwar dokar samar da muhalli mai kawar da duk wani shinge ga nakasassu, a ranar 1 ga watan Satumban bara. Sai dai zuwa yanzu, ko wannan dokar ta sa an samu biyan bukata?

LEADERSHIP